To fa: ‘Yan sanda sun kama mahaifina, yau ina cikin farin ciki – Cewar budurwa bayan ta gargadi mahaifinta akan kada ya fita yaki ji

0
126

Wata budurwa ta nuna farin cikinta matuka a lokacin da taji labarin cewa jami’an hukumar ‘yan sanda sun kama mahaifinta saboda ya karya dokar hana fita da gwamnati ta sanya.

Budurwar mai amfani da shafin sadarwa na Twitter ta bayyana cewa mahaifinta wanda bai ji gargadin da tayi masa ba a lokacin da yake shirin fita daga gida a jihar Legas. A cewar ta fitarshi keda wuya ‘yan sanda suka cafke shi.

“Yan sanda sun kama mahaifina yau, ina cikin farin ciki sosai, Na gaya mishi kada ya fita yaki jin magana ta, iyayenmu na Najeriya basa jin magana.”

Haka ita ma wata budurwa mai suna @King_Dija da tayi sharhi a kasan rubutunta ta ce, tana ganin ita ma abinda za ta yiwa mahaifinta kenan.

“Irin abinda mahaifina yake yi kenan shi ma, watarana sai na kira mishi NCDC, idan nace mishi ya zauna a gida baya zama. Amma lokacin da aka ce kowa ya fita, a lokacin ne shi kuma zai nuna yana son zaman gida.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here