Tirkashi: ‘Ya’yan El-Rufai sun caccaki Atiku Abubakar bayan dan shi ya tabo El-Rufai

0
557

‘Ya’yan Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, Bashir da Bello sun caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bayan daya daga cikin dan shi Mustapha ya tabo mahaifinsu.

Dan gidan Atiku, Mustapha wanda yayi martani akan maganar da El-Rufai yayi akan cewa iyaye su koyar da ‘ya’yansu tarbiyar girmama mata tun suna yara don kaucewa fadawa harkar fyade, ya bayyana maganar gwamnan Kaduna din a matsayin rainin hankali.

Bashir El-Rufai wanda yayi martani akan abinda Mustapha ya ce, yayi rubutu kamar haka:

“Lokacin da mahaifinsa Atiku Abubakar yayi magana akan cin hanci da rashawa, muma rainin hankali muka gani.

Shi kuwa Bello El-Rufai a nashi bangaren cewa yayi:

“Bash maganar ana yinta ne akan ganin darajar mata, ba wai kan ‘yan luwadi ake yi ba ko cin hanci. Kada kaga laifin sabon ango. Kada ka manta tsohon abokinka yana tunanin yanzu haka yana Villa tare da kusanci da NNPC!

Bello ya kara da kiran tsohon dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP a matsayin ‘Bobrisky din Adamawa’, ya ce:

“Duka dai ana magana ne akan hakkin mata. Barka da safiya. Tsohon abokina kuma sabon ango zai iya karbar nashi daga wajen Bobrisky din Adamawa.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here