Tirkashi: Yadda wani soja ya zazzagi shugaban hukumar Soji Tukur Buratai a sabon bidiyo

0
593

An kama wani jami’in hukumar sojin Najeriya da ya zagi shugaban hukumar sojin Najeriya, Tukur Buratai da sauran shugabannin tsaro na Najeriya a wani sabon bidiyo.

A bidiyon, sojan mai suna Lance Corporal Martins, ya ci mutuncin shugaban hukumar sojin Lt. Gen. Tukur Buratai, da sauran hafsoshin tsaro na Najeriya da suka ki daukar wani mataki akan kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a Najeriya.

A bidiyon mai tsawon minti biyu da dakika ashirin, Martins ya ce shugabannin tsaron Najeriya sun bawa Najeriya kunya. Ya caccaki shugabannin tsaron baki daya, musamman ma Buratai da shugaban ma’aikatan tsaro na kasa, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, da suka yi watsi da komai wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar.

Yayi zargin cewa hukumar ta sanya an kama wasu daga cikin sojoji da suka bukaci a basu kayan aiki masu inganci da za su yaki Boko Haram da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda a Najeriya.

Ya ce ya san da cewa za a kama shi koma a kashe shi akan bidiyon da yayi, amma ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwar shi ga kasar shi.

Ga dai bidiyon sojan a kasa:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here