Tirkashi: Uba ya hana danshi da ya dawo daga kasar waje shiga gidanshi yace sai an tabbatar masa da baya dauke da Coronavirus kafin ya kyale shi

0
110

Wata dirama da ta faru tsakanin uba da danshi ta jawo hankalin mutane da dama a jihar Ekiti bayan dan ya dawo daga kasar waje.

Mutumin wanda yake tsohon ma’aikacin hukumar kiyaye hadura ne wanda yayi murabus, ya bukaci dan shi ya cigaba da zama a Legas har zuwa lokacin da komai zai daidaita, amma dan bai ji maganar uban ba ya taho gida.

Da zuwan shi jihar Ekiti daga Legas, uban ya bukaci dole sai an gwada dan nashi ko kuma an killace shi na tsawon kwanaki 14 kafin ya barshi ya shigo masa gida.

Ya ce baya so ya zama daga cikin mutanen da zasu kara taso da matsalar ta Coronavirus a jihar Ekiti, kamar ma’aikaciyar lafiya mai shekaru 29 da ta mutu sanadiyyar kamuwa da cutar, bayan ta shigo jihar ta Ekiti daga jihar Legas inda take aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here