Tirkashi: Soja ya bayyana yadda abokin aikinshi soja ya yiwa mahaifiyarshi fyade

0
929

Wani tsohon jami’in hukumar soji na Najeriya, ya wallafa labarin shi mai ban tausayi na yadda soja ya yiwa mahaifiyarsa fyade a inda yake zama.

Da yake wallafa labarinsa a shafinsa na Twitter mai suna @FestusNG, tsohon sojan ya ce a lokacin da yake aiki da rundunar soji ta bataliya ta 146, mahaifiyarsa ta kai masa ziyara a lokacin a sansaninsu. Sai ya tafi ya barta da makwabcinsa wanda shi ma soja ne a lokacin, ai kuwa wannan sojan ya nemi hanyar da ya shiga cikin gidansa ya cakawa mahaifiyarsa wuka sannan yayi mata fyade.

“Fyade ba abu bane mai kyau. A lokacin da nake aikin soja da bataliya ta 146. Mahaifiyata ta ziyarce ni ta kai mini kayan abinci, ta dafa mana ta bawa duka abokanai na sojoji. Da misalin karfe 6 na yamma na tafi wajen aiki. Makwabcina ya shiga gidana ta cikin sili.

“Yana shiga ya cakawa mahaifiyata wuka sau biyu a baya sannan yayi mata fyade. Mahaifiyata ta shiga wani hali sosai a lokacin har tayi kokarin kashe kanta.

“A lokacin abin ya dame ni dole sai dana bar aikin sojan nan sannan na samu kwanciyar hankali. Idan har kayi tunanin yiwa wani fyade to ka tabbata cewa ka kuduri niyyar lalata mishi rayuwa ne.” Ya ce.

Post Source: @FestusNig Twitter Page

Press Lives ta kawo muku rahoton yadda shi kuma wani likita ya dora laifin fyade akan mata.

Likitan ya dora laifin a kansu ne inda ya ce yawanci shigar da suke yi ne ta sanya ake yi musu fyade.

Ya basu shawarar su dinga sanya kayan da za su rufe jikinsu, ma’ana kayan da za su rufe tsiraicinsu.

KU KARANTA: Shigar tsiraicin da kuke yi ne ya sanya maza ke yi muku fyade – Likita ya dora laifin fyade akan mata

Duka dai wannan na zuwa ne bayan fyade da aka yiwa dalibar jami’ar Benin aka kuma yi mata kisan gilla ba tare da sanin ko wane mai laifin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here