Tirkashi: Nura M. Inuwa yayi fashin baki akan halayen Malamai, Sarakuna, ‘Yan Siyasa da Mawaka

0
412

Wani rubutu da mawaki Nura M Inuwa ya wallafa a shafinsa ya ja hankalin mutane da dama, inda a ciki ya bayyana halayen mutane hudu da al’umma ke sauraron maganar su a duniya wadanda suka hada da Malamai, Sarakuna, ‘Yan Siyasa da kuma Mawaka.

Rubutun nasa ya jawo hankulan jama’a ne ganin duka abinda yayi magana a kai na da alaka da abubuwan dake faruwa a wannan lokacin, inda rubutun nasa yayi kama da hannunka mai sanda ga mutane amma cikin hikima, sai wanda ya lura zai gane.

Mawakin yayi rubutun kamar haka:

  1. Magana mai dadin ji da fadin gaskiya sai a bakin MALAM domin shi zai fada maka abin da Allah da Annabi suka fada ne ba nasa ba. ruwanka ka dauka ruwanka kaki.
  2. Iko da gadara da son girma a ayi hukunci da ka sai SARAKAI wannan tasa idan sun fadi magana koba gaskiya bace basu cika janyewa ba domin kada a raina su koda kuwa hukuncin ya sabawa abun da Allah da annabi sukace to su kuma mutuncin su suke kallo.
  3. Karya da yaudara hadama handama da babakere rashin sanin ya kamata tauye hakkin na kasa son kai da riya sai Dan SIYASA shine Wanda zai maka kyauta a daki yace amma sai an fita cikin jama’a zai baka.
  4. A mai da baki fari Sai MAWAKI yanaji yana gani za’a kawo masa haja mara kyau amma zai karbi tallanta inka matsa yace sana a yake a takaice ma dai mawaki shine mutumun da mutane suka gane bashi da akida. A fahimtata kenan amma inta saba da taka/ki ko kuma taku kuyimin Afuwa. 🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Wannan dai na zuwa ne a wannan lokaci da ake ta faman dambarwa da Sarkin Musulmai kan ajiye batun karin azumi daya a yau Asabar, amma kasancewar ya riga da ya bayar da umarnin a dauki azumi hakan bata samu ba baya ga ‘yan siyasa da suka siyasantar da lamarin annoba dake addabar duniya, haka su kuma Malamai na ta faman kira ga abinda Allah da Annabi suka ce, amma duk wanda fatawa ba tayi masa daidai ba sai ya kawo tawili a lokacin, inda su kuma mawaka kasuwar su ta bude suke rera wakoki ga wadannan azzaluman shugabanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here