Tirkashi: Miji ya yiwa matarshi mai dauke da ciki duka akan taki yarda ta zubar da cikin da yayi mata

0
311

An kwantar da wata mata a asibiti, bayan mijinta yayi mata dukan kawo wuka saboda ya bukaci ta zubar da cikin da yayi mata taki yarda ta zubar.

Matar mai suna Ronke Adeyemi, mai shekaru 33, wacce aka bayyana cewa tana dauke da cikin wata uku, ana zargin mijinta mai suna Bebu Abiodun Abbey, mai shekaru 35 da yi mata dukan tsiya a ranar Asabar 20 ga watan Yuni, a gidansu dake Ode-Irele, cikin jihar Ondo.

Dan uwan Ronke, Jimmy Adekanle, ya zargi cewa Bebu ya yiwa matarsa dukan tsiya, har ya sanya hannunshi a gabanta yana kokarin ganin ya zubar da cikin da karfin tsiya.

Ma’auratan sunyi aure a watan Agustan shekarar 2018, amma kuma aurensu dai gashi nan ne domin kuwa suna zaune ne cikin rikici kullum.

Jimmy Adekanle ya ce: “Kanwarmu tana ta kawo mana korafi a lokuta da dama akan yadda mijinta ke cin zarafinta tun bayan aurensu.

“A koda yaushe muna kokarin ganin mun daidaita su saboda mun san cewa aure dan hakuri ne, amma wannan karon laifin da tayi masa shine kawai saboda taki yadda ta zubar da cikin da yayi mata na wata uku.

“Mijin yana so ta zubar da cikin, saboda taki yarda ta zubar sai ya hau ta da duka, inda ya ji mata muggan raunika a jikinta.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here