Tirkashi: Matar aure ta cirewa mijinta azzakari da cizo bayan rikici ya hado su

0
1619

Wata mata mai shekaru 25 daga karamar hukumar Aboh Mbaise dake jihar Imo ta cirewa mijinta azzakari da cizo a yayin da rikici ya hado su.

Rahotannin da Daily Post ta ruwaito sun nuna ce ma’auratan suna da yara guda uku, maza biyu mace daya.

Dan uwan mutumin da lamarin ya faru da shi mai suna Udochukwu Nwimo ya ce tsohon saurayin matar ya zo a ranar Lahadi 31 ga watan Mayu ya dauke ta a babur bai dawo da ita gida ba sai can cikin dare.

Ya ce: ‘Tana shiga cikin gida, rikici ya barke tsakaninta da mijinta. Wasu makwabtansu ne suka fito suka raba su.

“Sai kuma da tsakar dare sai jin ihu suka yi, inda duka makwabtan sai da suka tashi, suna zuwa suka tarar matar ta cirewa mijin azzakari a lokacin da yake bacci.

“An wuce dashi zuwa asibiti, ban tunanin azzakarin shi zai kara aiki, saboda yadda ta cire shi abun babu kyawun gani,” ya ce.

Wani rahoto kuma da aka bayar ya bayyana cewa matar dama can ‘yar kwaya ce, kuma dama ta saba fada da mijin nata.

An dai mika matar zuwa ga hukumar ‘yan sanda, inda DPO, Ibiba Thom Manuel ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa matar ita ma ta samu raunika na cizo da yawa a jikinta, ciki kuwa hadda wanda yayi mata a nono.

Kamar yadda rahoton ya bayyana ma’auratan duka suna karbar magani a wani asibiti da ba’a bayyana sunan shi ba, inda su kuma jami’an ‘yan sanda ke cigaba da bincike akan lamarin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here