Tirkashi: Kalandar Mayan ta nuna cewa mako mai zuwa duniya za ta tashi

0
4432

A shekarar 2012, akwai jita-jita da ta dinga yaduwa na cewa duniya za ya tashi a ranar 21 ga watan Disambar shekara, hakan ya samo asali ne da yadda tsohuwar kalanda ta Mayan ta nuna a wancan lokacin.

A wancan lokacin har wani fim kamfanin fina-finai na kasar Amurka yayi mai suna Blockbuster, wanda yake nuni da cewa duniyar fa da gaske ta zo karshe. Inda a cikin fim din aka nuna yadda dutse mai aman wuta ya fashe baki daya, iska mai dauke da ruwa da wuta ta taso ta dinga kashe biliyoyin mutane. Amma duka wannan a iya fim dinne.

Idan har kana karanta wannan labari hakan na tabbatar da cewa wannan magana ta Mayan ba gaskiya bace.

Sai dai wani masani ya bayyana cewa akwai yiwuwar lokaci bai yi ba tukunna, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Masanin mai suna Paolo Tagaloguin, yayi lissafi dalla-dalla akan yadda kalandar Mayan da ta turawa take, inda wannan lissafi ya nuna cewa duniyar za ta tashi a mako mai zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

Haka kuma NASA ta ruwaito cewa akwai wata duniya mai suna Nibiru da ta tunkaro duniyar mu gadan-gadan, kamar dai yadda NASA din ta ruwaito.

Wannan abu dai an taba bayyana shi a shekarar 2003, cewar duniyar za ta zo karshe a wancan lokacin, bayan hakan bai yiwu ba sai aka matso da tashin duniyar zuwa shekarar 2012, inda aka danganta tashin duniyar da kalandar Mayan, wannan ma ba ta yiwu ba, to wannan dai shine karo na uku.

To mu Musulmai dama dai mun san wannan tatsuniya ce ta kanzon kurege, domin kuwa Qur’ani da Hadisai na manzon Allah sun bayyana dalla-dalla yadda duniyar za ta kare.

Amma hakan ba yana nufin kuma mu kara nesanta kanmu daga bautar Allah bane, domin kuwa koda duniya bata kare ba a yanzu, mutuwa tana nan, kuma tana iya daukar duk wanda kwanan sa ya kare.

A karshe muna addu’ar Allah yasa muyi kyakkyawan karshe ya kuma sa mu cika da imani.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here