Tirkashi: Jaruma Saratu Gidado ta tona asirin masu fyade na Najeriya

0
807

A yayin da kowa yake hawa shafukan sadarwa yake tofa albarkacin bakinsa dangane da masifar fyade da ta addabi al’umma a Najeriya. Sai gashi fitacciyar jaruma Saratu Gidado ta fito da na ta sabon salo.

Jarumar ta yiwa masu fyaden kaca-kaca a lokacin da ake daukar wani sabon shiri mai suna fyade, inda ta fito a matsayin lauya a cikin fim din.

An nunon jarumar a wani gajeren bidiyo mai tsawon minti biyu da ‘yan dakiku inda take yin tambaya ga masu fyaden take cewa:

“Wai ni tambayar da zanyi masu yiwa yara kanana da mata fyade, mai kuke ji ne idan kunyi musu? Neman da zaku yi musu ta karfin karfi, neman da zaku yi musu ba akan hanyar halal ba.

“Meye abin jin dadi akan fyade ta karfi? To mun gano sirrinku masu yin fyade, mun gano cewar kuna yi ne da niyyar kuna so kuyi kudi, bokaye sun baku sa’a to Allah ya tona asirinku.

“Mai zaku yi da wannan kudi? kudi na duniya da zaku mutu ku barshi, kudi da bana halal ba, ba zai yi albarka ba, saboda haka ku kiyaye, wallahi mun saka kafar wando daya da ku, duk mutanen da suke yiwa mata da kananan yara fyade wallahi sai inda karfin mu ya kare, za mu dinga yi muku addu’a sai kun wulakanta.

“Ni Saratu Gidado Daso, nayi alkawari na daura damara zanyi yaki da masu cin zarafin yara kanana da mata, nayi alkawarin masu yiwa yara kanana da mata fyade zamu dinga shari’a daku.

“Ubangiji Allah ya tsinewa duk mutumin da yake yiwa yara kanana da mata fyade, ya Allah ka wulakanta duk mutanen dake yiwa yara kanana da mata fyade, Allah ina rokonka ka tona asirinsu duk inda suke a boye ko a fili, Allah ka wulakanta su.” Cewar Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso.

Muhawara akan fyade dai tayi kamari, inda har ‘yan majalisu sun fara sanya baki akan gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki akan masu yin wannan aika-aika akan yara da mata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here