Tirkashi: Gwamnatin kasar Netherlands ta bukaci samari da ‘yammata suyi auren mutu’a yayin da ta sanya dokar hana fita

0
152
  • Gwamnatin kasar Netherlands ta shawarci marasa aure da su shirya yarjejeniya akan yin jima’i da juna
  • Gwamnatin ta bayar da wannan shawara ne a kokarin da take na rage yaduwar cutar Coronavirus a kasar
  • Ta ce ta san dole ne mutum ya bukaci jima’i a wannan lokacin hakan ya sanya ta shawarci duk mai bukata da ya daidaita da budurwa ko saurayi akan yadda zasu dinga saduwa da juna

Gwamnatin kasar Netherlands ta shawarci samari da ‘yammata marasa aure da su nemi abokanan yin zina ga wadanda suke bukatar hakan a wannan lokaci da ta sanya dokar hana fita.

Cibiyar lafiya ta al’umma dake kasar ta ce marasa aure suyi yarjejeniya a junansu idan har suna bukatar jima’i. A sanarwar da ta fitar a ranar 14 ga watan Mayu, ma’aikatar lafiyan ta bayyana cewa jima’i tsakanin masoya ya zama dole tunda babu yadda za ayi su kasa kusantar juna idan suna tare.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan mutane sun bayyana cewa babu wata shawara da aka bawa marasa auren a kasar, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Cibiyar ta ce: “Dole ne mutumin da bashi da aure yaji yana son yin jima’i a wannan lokaci da aka hana zirga-zirga.” Saboda haka dole mu dauki mataki domin rage yaduwar cutar Coronavirus, marasa aure suyi yarjejeniyar saduwa da junansu.

“Kuyi yarjejeniya yadda zaku iya yin jima’i da junanku,” cewar cibiyar lafiya ta kasar.

“Misali ka samu wanda kake so kayi jima’i dashi, idan har kai lafiyarka kalau.

“Kuyi magana ta fahimta, ya bayyana maka yawan mutanen da ya hadu dasu, kai ma haka, yanayin yawan mutanen da kuka hadu dasu yanayin yiwuwar yaduwar cutar a junanku.”

Haka kuma cibiyar ta shawarci ma’auratan da suke kokwanton cewar abokin rayuwarsu ya dauki cutar.

“Kada ku sake ku kwanta da duk wanda kuke tunanin yana dauke da cutar.”

Kasar ta Netherlands na kulle tun ranar 23 ga watan Maris, inda aka sanya dokar barin iya mutum uku a gida daya kawai, a hakan ma da dokar dole sai sun nesanci juna.

A ranar 11 ga watan Mayu dinnan ne dai gwamnatin kasar ta amince da bude wasu wurare a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here