Tirkashi: Ango ya gano cewa amaryar da ya aura katon gardi ne kwanaki biyu da yin aure

0
4846

Labarin dan kasar Indonesia mai suna Muh wanda ya saki matarsa kwanaki biyu da yin aure bayan ya gano cewa katon gardi ne ya yadu a shafukan sadarwa.

An ruwaito cewa Muh ya hadu da matarsa Mita a shafin Facebook kimanin wata daya da ya wuce, inda suka fara soyayya a shafin sadarwa.

Masoyan sun hadu a gaske, inda suka fita yawon shakatawa tare, shi kuwa Muh da bai san meke faruwa ba tuni ya fada kogin soyayyar Mita, wacce ya bayyanata da ‘kyakkyawa kuma mai mutunci.’

Bayan shafe makonni suna soyayya, sai ya nuna yana son aurenta, ai kuwa sai ta amince cikin gaggawa.

Muh da Mita | Photo Source: Oddity

Muh mai shekaru 31 sai ya sanar da iyayenshi shirin da yake yi na auren Mita. Iyayenshi suka je gidansu Mita suka kai kudin sadaki. Inda suka bayar da Rupiah miliyan 20, kimanin N555,000 a kudin Najeriya, iyayen yarinyar suka yi murna da wannan sadaki.

Masoyan an daura musu aure a ofishin harkokin addini dake Kediri, cikin Central Java dake kasar ta Indonesia a ranar 2 ga watan Yuni.

Duk da dai amaryar mai shekaru 25 fuskarta a rufe take a ranar wannan biki, babu wanda yayi tunanin cewa bata da gaskiya. Ai kuwa wannan aure nasu ya samu halartar manyan malaman addini daga yankuna daban-daban, kuma duk cikinsu babu wanda yayi zargin akwai wata makarkashiya a kasa.

Shi kanshi ango bai yi zargin komai ba a lokacin da amaryar shi taki amincewa ta kwanta dashi a darensu na farko.

Sai dai ya fara zargin wani abu a lokacin da ya nemi kwanciya da ita a karo na biyu taki amincewa.

Mita | Photo Source Oddity

Bayan dare na uku ya wuce ba tare da ta kyale shi ya kwanta da ita ba, sai Muh ya fara gabatar da bincike akan amaryar tashi, ai kuwa yayi mamaki sosai da ya gano cewa Mita katon gardi ne.

Ba a bayyana yadda aka yi Mita ta gano cewa mijinta ya gano cewa ita katon gardi bane, amma dai kawai lokacin da Muh ya dawo gida tuni har ta gudu daga gidan.

Cikin fushi Muh ya bayyanawa dangin shi gaskiyar lamarin, ya kuma sake ta cikin gaggawa.

Wannan abu da ya faru da shi ya sanya ya kai kara wajen ‘yan sanda da korafin cewa wannan katon gardi ya yaudare shi.

‘Yan sanda sun gano saurayin sun kuma kama shi, inda aka gano cewa ainahin sunansa shine Adi. Ba a bayyana ko za ayi masa hukunci ba a cikin rahoton.

Wannan aure na Muh da Mita ya zama na farko a tarihin aurace-aurace a kasar ta Indonesia.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here