Babbar kotun jihar Ondo ta yankewa wani babban fasto mai suna Fasto Kolawole Samson hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin kashe wani yaro a wani kauye kusa da Okeigbo.

Kotun wacce ke zama a Akure da mai shari’a Ademola Bola ke jagoranta ta kama faston da laifin saran yaron da adda a kanshi a gonar da faston yake kiwon kifi a watan Maris na shekarar 2016, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Marigayin mai suna Olaniyi an bayyana ya fita kamun kwadi ne tare da abokananshi guda uku a wajen da faston yake kiwon kifi a lokacin da lamarin ta faru.

A wani rahoton kuma wani mutumi mai suna Victor Edet ya bayyana cewa dan gidan fasto Enoch Adeboye yana shiga irinta ‘yan daba.

Mutumin ya wallafa hotunan dan gidan faston a shafinsa na Facebook, inda aka nuno dan gidan faston sanye da kaya wadanda basu kamata ba.

Mutumin ya ce yayi matukar mamaki da ganin wannan hoto, inda yake tambaya daga yaya fasto zai yi shiga irin wannan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here