Tirkashi: An yanke masa hukuncin shekaru 12 a gidan yari kan ya gogawa karuwai 3 cutar kanjamau bayan yayi lalata da guda 12 a lokaci daya

0
258
Nehemiah Rodney | Source: Mail Online

An yankewa wani mutumi hukuncin shekaru 12 a gidan kaso bayan ya gogawa wasu karuwai guda uku cutar kanjamau, bayan yayi zina da guda 12 a lokaci daya.

Mutumin mai suna Nehemiah Rodney, mai shekaru 61 dake zaune a Swidon, an same shi dauke da cutar a watan Agustan shekarar 2013, amma ya cigaba da zina da mata ba tare da amfani da abin kariya ba, wato kwaroron roba.

Jami’an ‘yan sanda sun bayyana cewa sun fara bicike akan shi tun a shekarar 2017, bayan sun samu wani korafi daga wata mata da aka sameta dauke da cutar, bayan tayi lalata da shi.

Sai dai kuma Rodney ya musanta wannan zargi da ake masa, inda yace shi babu wata mace da ya gogawa cutar.

A rahoton da Mail Online ta ruwaito a ranar Laraba, ta bayyana cewa kotun Bristol Crown, ta gano cewa Rodney yayi lalata da mata da yawa a cikin ‘yan shekarun nan ba tare da ya sanar da su cewa bashi da lafiya ba.

Rahoton ya bayyana cewa jami’an tsaro da jami’an lafiya sun gana da sama da mata guda 50 da ake tunanin ya hada alaka da su.

Haka kuma kotu ta gano cewa Rodney baya shan maganin zai rage karfin cutar da zai sa wasu baza su dauka ba.

Charles Thomas, wanda ya gurfanar da Rodney, ya ce jami’an lafiya sun bayyana cewa bayan tambayarshi ya kasa bayyana yawan matan da ya kwanta da su.

Wani bincike da jami’ar Oxford tayi ta bayyana cewa a takaice Rodney ya gogawa mata guda uku cutar ta kanjamau.

Matan guda ukun da ake ganin sun kamu da cutar sun yi lalata da Rodney a shekarar 2015 da shekarar 2016. Biyu daga cikinsu sun san shi tun suna matasa.

A lokacin da ake sauraron karar tashi, daya daga cikin matan ta bayyana cewa bayan ta gano tana dauke da cutar tayi kokarin kashe kanta.

A lokacin da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya bayyana cewa ya yankewa Rodney hukuncin shekaru sha biyu da rabi a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here