Tirkashi: An sanya fim din batsa a wajen taron majalisar kasar Afrika ta Kudu

0
237

Taron bidiyo na yanar gizo da ‘yan majalisar kasar Afrika ta Kudu suke yi ya samu tsaiko bayan masu kutsen yanar gizo sun haska hotunan batsa a wajen taron.

Majalisar kasar dai an rufeta inda aka koma taro a yanar gizo sanadiyyar dokar hana zirga-zirga da aka sanya a kasar sakamakon annobar Coronavirus da ta addabe su.

A jiya Alhamis 7 ga watan Mayu, ‘yan majalisar kasar sun samu matsala a lokacin da suke gabatar da taro a yanar gizo, bayan masu kutsen yanar gizo sun haska hotunan batsa a lokacin da suke gabatar da taron.

Wata mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter mai suna Natasha Ntlangwini ta wallafa yadda lamarin ya faru a shafinta, inda ta nuna bacin ranta akan yadda gwamnatin kasar ba ta da wata hanya da za ta iya hana abu irin wannan ya faru a kasar, inda ta ce:

“Masu kutsen yanar gizo sun sanya bidiyon batsa a wajen taron ‘yan majalisarmu yau da safe. Wannan abin kunya ne ace bamu da wata hanya da zamu iya hana abu makamancin haka ya faru a kasar mu.”

Masu kutsen kuma sun aika da kalamai na zagi da cin mutunci ga shugabar taron Thandi Modise, wacce take ita ce Kakakin majalisar kasar.

Modise ta ce sai da tayi gargadi akan amfani da manhajar Zoom wajen gabatar da wannan taro na yanar gizo.

Anyi niyyar wallafa wannan taro a gidan talabijin na kasar ne, amma komai ya dakata yayin da wannan lamari ya faru. Inda tilas ta sanya ‘yan majalisar suka koma amfani da wata manhajar wajen gabatar da wannan taro nasu.

Wannan dai ba shine karo na farko da irin haka ta faru a kasar ta Afrika ta Kudu ba, inda watan da ya gabata, wani taron yanar gizo na mata da aka gabatar a kasar shima anyi abu makamancin haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here