Tirkashi: Almajirai 193 sun kamu da Coronavirus a jihar Kano

0
307

Almajirai 193 ne suka kamu da cutar Coronavirus a jihar Kano, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Da yake magana a wajen taron COVID-19 da aka gabatar jiya 2 ga watan Yuli a jihar Kano, kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Mohammed Kiru ya bayyana cewa a yanzu haka akwai 1,860 da aka killace a sassa guda uku na jihar, inda aka samu 193 da suke dauke da cutar.

Sanusi wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gwamnatin jihar ta yiwa tsarin almajiranci kwaskwarima, ya ce 86 daga cikinsu an samu cutar a jikinsu a wajen killace na Gabasawa, 68 a Karaye sai kuma 38 a Kiru.

Ya nuna farin cikinsa kan tsarin killace almajirai da jihar ta ke yi, inda ya kara da cewa inda gwamnatin ba tayi da gaske wajen yaki da cutar ba da tuni lamarin ya wuce yadda ake tunani da an barsu sun cigaba da yawo a gari.

Ya tunatar da cewa ya zuwa yanzu, jihar ta mayar da almajirai 1,183 zuwa jihohin dake makwabtaka da jihar irin su Jigawa, Kaduna, Katsina, Gombe, Bauchi, Kebbi da Zamfara, bisa la’akari da shawarar kungiyar gwamnonin Arewa, na kawo karshen barace-barace a tituna.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kirkiri makarantun kwana na almajirai guda uku don fara daukar dalibai almajirai na jihar Kano, yana mai cewa wadannan makarantu suna cikin Bunkure, Bagwai da kuma karamar hukumar Madobi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here