Tirkashi: Akuya da gwanda sun kamu da cutar Coronavirus a kasar Tanzania

0
279

A jiya Lahadi ne, shugaban kasar Tanzania, John Magafuli, ya bukaci a gabatar da bincike akan kayan aikin cutar Coronavirus na kasar bayan an gabatar da gwaji akan akuya da gwanda an samu kwayar cutar a jikinsu.

Da yake magana a wajen taro a Chato a yankin arewa maso yammacin kasar, Magafuli ya ce akwai yiwuwar akwai matsalar na’ura a jikin kayan aikin da aka kawo su daga kasar waje.

Shugaban kasar yace ya sanya hukumomin tsaron kasar su binciki kayan aikin don tabbatar da ingancinsu.

Shugaba Magafuli ya bayyana hakane bayan kayan aikin sun bayyana cewa gwanda, akuya da tinkiya suna dauke da kwayar cutar ta Coronavirus, inda kuma na’urar ta bawa wadannan abubuwa sunayen mutane hadda shekaru.

Shugaba Magafuli ya ce tunda har wannan na’ura ta bayyana cewa akuya da gwanda na dauke da wannan cuta, akwai yiwuwar mutane da yawa da aka yi musu gwaji aka bayyana suna dauke da cutar, akwai yiwuwar basu da ita.

“Mun gabatar da gwaji akan gwanda da akuya, ya bayyana kuma suna dauke da wannan cuta, hakan na nuni cewa akwai matsala a wani wajen,” ya ce.

“Shin yanzu zamu fara killace dabbobi da ‘ya’yan itatuwa ne?” tambayar shugaba Magafuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here