Tinubu da Igbo ba za su taba yin mulkin Najeriya ba – Miyetti Allah

0
537

A ranar Asabar din nan da ta gabata ne shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa, Abdullahi Bodejo, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba zai taba hawa kujerar shugaba Buhari ba a zaben da za a gabatar na 2023.

Haka kuma Abdullahi Bodejo ya bayyana abinda zai saka yayi matukar wahala ga dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a Najeriya.

Bodejo ya ce bai yadda a dinga karbebeniya ta mulki tsakanin Kudu da Arewa ba, sakamakon abubuwan da ake yiwa ‘yan Arewa a wasu yankuna na Najeriya.

A cewar shi: ‘Tinubu da ‘yan kabilar Igbo ba za su taba mulkar Najeriya ba. Ko kun san cewa idan kuka je wasu yankunan na Kudancin Najeriya, idan suka ga Hausa, suna kiran shi da Dan Boko Haram ne, ko kuma su ce ‘Onye Hausa’.

“Wannan nau’i na rashin tausayi yana zuciyarsu. Zai yi wahala Igbo su mulki Najeriya saboda babu wani abu na kirki a zuciyar su.

Da aka tambaye shi ko ya san shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai lashe zaben 2015 ba ba tare da Bola Tinubu ba, sai ya ce: “Na riga na sanar daku 2015 ta zama labari yanzu. Abinda kawai na sani shine Tinubu ba zai iya zama shugaban kasa a Najeriya ba. Ya tsufa sosai, mai yiwuwa ya girmi shugaba Buhari. Wasu na ganin cewa shine shugaban Yarabawa, amma ba shi bane,” in ji shi.

Haka kuma Press Lives ta kawo muku rahoton yadda shima shugaban kungiyar matasan Arewa, Yerima Shettima ya sha alwashin cewa baza su taba bari Igbo ya mulki Najeriya ba saboda basu da amana.

KU KARANTA: Ba za mu taba bari Igbo ya mulki Najeriya ba, saboda basu da amana – Yarima Shettima

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here