Tashin hankali: Shekara 7 kenan ina zina da ‘ya’yana mata tun bayan mutuwar matata

0
4508

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, wani mutumi mai shekaru 50, mai suna Peter Ayemoba, ya shiga hannun ‘yan sanda, bayan kama shi da laifin zina da ‘ya’yan da ya haifa.

Ayemoba ya bayyanawa ‘yan sanda cewar ya shafe shekaru bakwai yana kwanciya da ‘ya’yan nashi tun bayan mutuwar matarsa.

Ya ce kwanciya da ‘ya’yan nashi yakan sa yaji kusanci tare da matarshin, ya ce kuma hakan yasa yake jin soyayyar ‘ya’yan shi sosai a zuciyarshi.

Ayemoba ya ce: “Na fara kwanciya da ‘ya’yana shekaru bakwai da suka wuce, a lokacin da matata ta mutu a shekarar 2013.

“Mutuwarta ta sanya ni cikin wani hali sosai, hakan yasa ban ma san lokacin dana fara kwanciya da ‘ya’yan nawa ba, maganar gaskiya ban ma san abinda ya shiga kaina ba.

“Nayi zargin ko wani ne yayi mini asiri, saboda abinda nayi shekaru bakwai da suka wuce, ba abu bane da kwakwalwa za ta iya yadda dashi.

“Na dinga kusantar ‘ya’yan nawa bayan mutuwar matata, har ta kai ga har sai dana fara kwanciya da su.

“Maganar gaskiya bazan iya bayyana ainahin abinda yasa nake yin haka ga ‘ya’yana ba. Amma wani abu a zuciyata ya cigaba da rada mini cewa ba ni kadai ne mutumin da ya fara kwanciya da ‘yarshi ba, kada na damu kwata-kwata.”

Ayemoba ya bayyana cewa ya samu amincewar ‘ya’yan nasa kafin ya fara kwanciya da su, ya kara da cewa kuma amincewar sun ne ya saka hatta bayan ya auro wata mata ya cigaba da kwanciya da su.

Ya ce: “Bayan binne matata na fara jin soyayyar ‘ya’yana a cikin zuciyata. Na fara zuwa dakinsu na fara wasa da su, har ta kai ga na fara kwanciya da su daya bayan daya amma da amincewar su.

“Duk lokacin da suka ki amincewa da bukatata, sai nace musu ina so na kara samun kusanci da sune tunda mahaifiyarsu bata nan.

“A wasu lokutan nakan yi musu barazanar kisa, ko kuma nace musu zan kashe kai na idan basu amince na kwanta da su ba.

‘Na sanar musu da cewa jima’i tsakanin ‘ya’ya da uba ba komai bane, hatta a Bible an rubuta haka.

Mutumin da yake da ‘ya’ya guda shida ya bayyana cewa sabuwar amaryarsa bata san da cewa yana kwanciya da ‘ya’yan nasa ba.

Ya ce ‘ya’yan nasa kuma basu sanar da matar tasa ba saboda babu jituwa tsakaninsu.

Ya ce: “Ya’yan nawa sun gano cewa abinda nake yi bai dace ba, sai suka tilasta na auro wata matar don ta dinga biya mini bukatata, amma duk da auren, ina kwanciya da su a lokuta da dama idan na samu dama.

Bayan sun gaji da zina da mahaifin nasu yake yi dasu, ‘ya’yan sun kai karar mahaifin nasu wajen danginsu, inda su kuma suka sanar da ‘yan sanda.

Ayemoba ya ce yayi mamaki akan abinda ‘ya’yan nashi suka yi masa.

Ya ce: “Abinda ya bani mamaki shine duk wannan shekaru da muka kwashe duk kwanciyar da nake yi da su, muna cikin farin ciki a koda yaushe, amma kawai sai suka kai karata. Har yanzu ina mamakin abinda suka yi.”

“Amma ina ganin lokaci nane yayi, saboda haka a shirye nake doka tayi aiki a kaina.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here