Tashin hankali: Saurayi ya yiwa dan uwanshi gunduwa-gunduwa da adda akan mangwaro

0
207
  • Wani saurayi mai suna Chinedu ya shiga hannun hukumar ‘yan sanda a jihar Abia, bayan kama shi da laifin kisan kai
  • Saurayin dai ya kashe dan uwanshi ne akan mangwaro da ya hado su rikici
  • An ruwaito cewa yayi amfani da adda ne wajen sassara dan uwan nashi saboda yaje yaji dalilin da ya saka ya dakar masa da

Jami’an hukumar ‘yan sanda na jihar Abia sun tabbatar da kama wani saurayi mai suna Chinedu Omeonu wanda ya kashe dan uwanshi mai suna Solomon Monday Orji, a Mgboko Umuoria, cikin karamar hukumar Obingwa.

An gano cewa daya daga cikin ‘ya’yan Orji, yaje gidan kawunshi Chinedu Omeonu domin ya tsinto mangwaro da suka fado.

Omeonu ya naushi karamin yaron dan gidan Orji, inda yayi masa dukan tsiya da har sai da ta kai ga ya suma.

Orji ya garzaya gidan dan uwan nashi domin yaji dalilin da ya saka ya yiwa dan shi irin wannan duka na rashin imani.

Omeonu wanda ranshi ya baci akan tinkararshi da Orji yayi kan dakar masa da, ya dauki adda ya dinga saran Orji da ita a lokacin da yake shirin fita daga gidan shi.

An ruwaito cewa Orji ya mutu a take a wajen, bayan Omeonu ya sassare shi da addar.

Sai dai bayan matasa sun gano sun yiwa Omeonu dukan tsiya kafin su danka shi a hannun ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Abia, Geoffrey Ogbonna, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyanawa jaridar Linda Ikeji cewar za su gurfanar da mai laifin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike a kanshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here