Tashin hankali: Saurayi ya kone kanwarsa kurmus saboda ta mari mahaifiyarsu

0
611

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wani saurayi mai suna Chima da laifin kone kanwarsa mai suna Victoria, a gidansu dake CAC Bus Stop, Okokomaiko, Ojo a ranar 14 ga watan Mayu.

A yadda rahoton ya nuna, Chima ya yiwa kanwarsa Victoria cikin wata biyu, inda suke sana’ar sayar da abinci.

Rikicin ya samo asali a lokacin da mahaifiyarsu ta daki Victoria akan tana fita daga gida taje ta hadu da wasu maza a titi. A wannan lokacin rikici ya barke tsakaninsu har Victoria ta daga hannu ta mari mahaifiyarsu. Shi kuma wannan abu ya bata masa rai sosai, sai yaje ya dauko jarkar man fetur ya kwarawa Victoria ya sanya mata wuta, hakan ya sa ta kone sosai.

Anyi gaggawar garzayawa da Victoria zuwa asibiti mafi kusa, amma likitocin suka ki karbata. Daga nan aka kai ta asibitin Alimosho dake Igando, inda a nan likitoci suka bayyana cewa ta mutu.

An bayyana cewa Chima yayi kokarin guduwa bayan ya gano abinda ya yiwa kanwar ta shi, amma matasan unguwarsu suka kama shi, inda suka mika shi ga jami’an ‘yan sanda.

Mahaifiyarsu da tayi kokarin kashe wutar da ta kama Victoria ita ma ta samu konewa a wurare da dama a kafarta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce sun mika Chima zuwa ofishin binciken manyan laifuka dake Yaba domin cigaba da bincike a kanshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here