Tashin hankali: Samari 5 sun bawa budurwa kwaya kowannensu yayi zina da ita a jihar Kaduna

0
252

Wata mai amfani da shafin sadarwa na Twitter ta zargi ‘yan sanda da nuna halin ko in kula bayan an yiwa wata budurwa ‘yar shekara 18 fyade a jihar Kaduna, bayan abokananta maza guda biyar sun bata kwaya ta sha.

Sai da aka kwantar da budurwar bayan sun gama amfani da ita, inda biyu daga cikin wadanda suka yi mata fyaden kuma aka kulle su a ofishin ‘yan sanda. Sai dai kuma sauran guda ukun sun boye inda ake tunanin iyayensu na da hannu wajen boyesu.

Haka wacce ta wallafa rubutun a shafinta na Twitter ta bayyana cewa iyayen samarin da suka yiwa yarinyar fyaden suna so a janye maganar baki daya, inda ta bayyana cewa sunce zasu biya kudi domin a mance da maganar.

Haka kuma ta bayyana cewa ‘yan sanda suna ta karbar kudi a hannun iyayen yarinyar suna ta jan maganar tsawon makonni.

A cewar wata kuma da ta bayyana ta san yarinyar da aka yiwa fyaden ta bayyana cewa lamarin ya taba kwakwalwar yarinyar, inda take nuna alamun kamar ta samu tabin hankali. Haka kuma tana ta suma tun bayan lokacin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here