Tashin hankali: Sama da mutum 40,000 sun kamu da cutar Coronavirus cikin kwanaki 4 a kasar Rasha

0
178

Alamu na nuni da cewa kasar Rasha na neman kama hanyar zama sabuwar cibiyar cutar Coronavirus, ganin yadda dubunnan mutane ke kamuwa da cutar a kowacce rana a kasar.

A yau Larabar nan hukumar lafiya ta kasar ta bayyana cewa an samu karin mutum 10,559 da suka kamu da cutar a cikin kwana daya kacal.

Karin mutane sama da dubu goman da aka samu ya kara yawan mutanen da suke dauke da cutar ya kai mutum 165,929, inda mutum 1,537 suka mutu daga cikinsu.

Ya zuwa yanzu dai kasar Rasha ta zama kasa ta biyar a nahiyar Turai da cutar ta Coronavirus tafi yin ta’adi a cikinsu, banda kasar Spain, Italiya, Birtaniya da kuma kasar Faransa.

Bayanai sun nuna cewa tun daga ranar 3 ga watan Mayun nan, mutane sama da dubu goma ne ke kamuwa da cutar a kowacce rana.

Sai dai kuma duk da yawan kamuwa da cutar da ake yi, har yanzu cutar ba ta fara barnar kashe al’umma ba a kasar ta Rasha, kamar yadda kasashen Amurka, Italiya, Spain, Birtaniya da sauransu suke fama da asarar rayuka a kowacce rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here