Tashin hankali: Sama da mutum 10,000 sun kamu da cutar Coronavirus cikin sa’a 24 a kasar Rasha

0
149

Hukumomi a kasar Rasha sun bayyana cewa mutum dubu goma ne cutar Coronavirus ta harba cikin awanni 24 a kasar.

Wani bincike da ma’aikatar lafiya ta kasar ta gabatar a kwanan nan, ya nuna cewa yawan mutanen da cutar ta harba ya zuwa yanzu a kasar ya kai kimanin mutum 123,54, bayan kuma wasu sababbin mutane 9,623 da cutar ta kama a cikin sa’a 24.

Rahotanni sun bayyana cewa a iya birnin Moscow kawai an samu karin mutane 5,358 da suka kamu da cutar a kwana daya, inda yawan mutanen da suke da ita a birnin ya kai 62,658.

A yanzu haka Firaministan kasar ta Rasha Mikhail Mishustin, ya shiga cikin jerin manyan mutane na duniya da suka kamu da cutar ta Coronavirus.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta kashe mutum 1,222 a kasar ta Rasha tun bayan shigar ta kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here