Tashin hankali: Mata ta kashe mijinta ta yanke mazakutarsa bayan ta gano yana soyayya da babbar kawarta a jihar Nasarawa

0
171

Wata mata mai shekaru 33 mai suna Janet Ekpe daga jihar Nasarawa ta kashe mijinta da suka shafe shekaru takwas suna tare, bayan ta gano cewa yana soyayya da babbar kawarta mai suna Hellen, a garin Zumbagwe cikin karamar hukumar Karu dake jihar Nasarawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Janet da Sunday suna da yara guda biyu, kuma suna zaune cikin farin ciki, har zuwa lokacin da ta gano cewa Sunday ya fara baya-baya da ita bayan sun haifi yaro na biyu.

A cewarta farkon aurensu mijinta na matukar son jima’i, hakan ya sanya ita ma ya koya mata. Ta ce amma lokacin da taga ya fara baya-baya da ita ta shiga damuwa, inda daga karshe ma ya daina kwanciya da ita baki daya.

Bayan ta gabatar da bincike ta gano cewa mijin nata yana kwanciya da babbar kawarta ne mai suna Hellen wacce take bazawara ce. Janet ta bayyana cewa ta taba gayawa kawayenta irin karfin da mijinta yake dashi a gado, har wasu daga cikinsu suka bukaci ta ara musu shi suma su kwanta da shi.

Janet ta ce tazo matsayin da ta gaji da uzurin da yake bata akan abinda yasa baya son kwanciya da ita. Ta ce akwai lokacin da mijinta ya taba gaya mata ta dinga tunano lokacin da suka kwanta tare domin ta dinga biyawa kanta bukata.

Janet ta ce watarana kawai taji ranta ya baci sai ta yanke shawarar kashe shi saboda irin bakin cikin da yake sanya mata. Ai kuwa sai ta sanya masa guba a abinci ta tsaya tana kallon shi ya mutu. Sannan kuma sai da ta tabbata ta yanke masa mazakuta bayan ya mutu.

Kawun marigayin mai suna Adakole Onoja, da aka yi hira da shi ya ce yasha kiran Sunday a waya akan kada ya dinga barin matarshi ba tare da yana kwanciya da ita ba, bayan matar ta kai mishi karar abinda ke faruwa tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here