Tashin hankali: Masu cutar Coronavirus sunyi garkuwa da likitoci biyu a Kano

0
1044

A jiya Alhamis 7 ga watan Mayu ne, masu cutar Coronavirus da aka killace a Kwanar Dawaki, suka yi garkuwa da wasu likitoci guda biyu mace da namiji.

Tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano, Farfesa Aminu Mohammed, shine ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yayi hira da Wazobia FM, yau da safe.

Yace ma’aikatan lafiyan sun fada hannun masu coronavirus dinne a lokacin da suke zagayawa suna duba su, inda suka kullesu na tsawon sa’a hudu.

Aminu ya ce likitocin sun sha wahala kafin su samu su karya kofar dakin da aka kulle su suka fito daga ciki da kyar.

Daya daga cikin marasa lafiyan da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa suna zanga-zanga ne akan jinkirin da ake yi musu na bayyana musu halin da suke ciki, inda aka tsare su ana basu magani tsawon mako daya babu labari.

Sai dai kuma yace ma’aikatan lafiyan da aka kulle din ba balla kofar suka yi ba, sun bude su da kansu ne bayan shugaban ma’aikatan lafiyar wajen ya sanya baki akan lamarin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here