Tashin hankali: Kwarankwatsa ta kashe jami’an FRSC guda 3 yayin da suke kan aiki

1
454

Jami’an hukumar kiyaye hadura na Najeriya guda uku sun ce ga garinku nan bayan kwarankwatsa ta fado musu a jihar Ogun dake Kudancin Najeriya.

Lamarin ya faru a safiyar ranar Laraba, 17 ga watan Yuni, a wani kauye mai suna Ilese dake karamar hukumar Ijebu North-East cikin jihar ta Ogun.

Kwarankwatsar ta fado kansu da misalin karfe 10 na safe, yayin da jami’an hukumar ta kiyaye hadura suke shirin fita wajen aiki.

A rahoton da Vanguard ta fitar, wani babban jami’i a cikinsu ya bayyana cewa su kimanin goma sha biyu ne suke aiki a wajen a cikin ofishi guda daya a lokacin da aradun ta fadowa uku daga cikinsu.

Sai dai bayan faruwa lamarin, wasu jami’an tsaro na jihar da ake kiransu da suna ‘OP MESA’ sun cigaba da lura da wajen, inda suka kori mutanen dake wajen suna kallon lamarin, sannan suka hana ‘yan jarida daukar hotunan lamarin.

Haka kuma, masu ibadar gargajiya a yankin da aka fi sani da Sango sun shiga cikin jami’an hukumar FRSC din, domin yiwa gawarwakin addu’a kafin a kai su ga gwamnati ayi shirin binne su, cewar rahoton.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here