Wani saurayi ya koyi darasi a wajen wata karuwa, bayan tayi garkuwa dashi take yi masa barazana da wuka, bayan yayi lalata da ita yaki biyanta kudin da suka yi yarjejeniya.
Ita dai kamar abin bai dame ta ba, domin kuwa karuwar ta wallafa wannan abu nasu a shafinta na Facebook kowa ya gani.
Karuwar ta nuno saurayin a bayan motarta inda yake rokonta ta yafe masa, ita kuwa tana yi masa tsawa akan ya rufe mata baki kafin ta sauke masa bala’in dake kanta.
Mutumin yayi kokarin boye fuskarsa daga bidiyon da take dauka amma ina ya makaro domin kuwa har ta riga ta dauka kafin ya rufe fuskar ta sa.