Tashin hankali: Kare yayi kalace da uwargidanshi ya aikata kiyama

0
132

An iske gawar wata mai shekaru 52 mai suna Lisa Urso, a cikin gidanta dake Illinois bayan karenta ya kasheta.

Rahotanni sun bayyana cewa kwanan nan Lisa ta karbo karen, inda hukumomi suka bayyana mata cewa babu abinda aka koya masa in ba fada ba.

An tsinci gawarta a bayan gidanta a ranar Asabar da yamma.

A yadda rahoton ya nuna karen ya sha kai wa saurayinta hari a lokuta da dama. ‘Yan sanda sun bayyana cewa karen ya kasheta a cikin gidanta, kuma lokacin da ya kasheta saurayin nata baya nan. Jami’an tsaron sun bayyana cewa karen ya kware matuka wajen fada da ‘yan uwansa karnuka.

“Ba a wuya ya cije ta ba, yawancin cizon da yayi mata a kafa ne da hannu,” cewar Dr Howard Cooper.

Kafin mutuwarta, Lisa tana daya daga cikin masu fafutukar kare hakkin dabbobi na kasar Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here