Tashin hankali: Dalibar jami’a ta mutu a dakin saurayi

0
624

Wata dalibar jami’ar tarayya ta Oye Ekiti, mai shekaru 21, wacce ta ziyarci saurayinta a dakinshi dake kwalejin jihar Osun, an iske gawarta a cikin dakin nashi.

Kamar yadda VoiceAirMedia ta ruwaito sunan budurwar Faderera Oleyede.

An samu gawar budurwar a dakin saurayinta a yankin Koko dake garin Iree cikin karamar hukumar Boripe, dake jihar Osun.

Saurayin shima an bayyana sunanshi da Maliki Ayo, wanda yake dalibi ne a kwalejin jihar ta Iree.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabanshi, kuma ya roki a boye sunanshi, marigayiyar taje dakin saurayin tare da kawarta suka kaiwa saurayin wanda yanzu ake nema ruwa ajallo aka rasa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Opalola Yemisi ya ce tuni an kai gawar marigayiyar zuwa dakin ajiye gawa domin gabatar da gwaji.

Yemisi ya bayyana cewa kawar budurwar da suka je dakin saurayin tare mai suna Adekemi Adewumi an kamata, kuma ta tabbatar da cewa sun ci abinci tare da daddare.

Sai dai ta ce ‘yan sanda suna cigaba da bincike akan lamarin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here