Tashin hankali: Ango ya yiwa amarya fyade ta mutu, kwana 20 da yin aurensu a jihar Jigawa

0
738

Wani mutumi mai shekaru 30 a duniya mai suna Alasan Audu, an ruwaito cewa ya yiwa amaryarsa fyade bayan taki barinshi ya kwanta da ita kwanaki 20 da yin aurensu.

An ruwaito cewa Audu ya yiwa matarsa mai shekaru 17 a duniya, mai suna Hansa’u fyade a ranar 21 ga watan Afrilu, a kauyen Kankarelu dake karamar hukumar Ringim cikin jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis, ya ce amaryar tana da wani wanda take so ta aura, amma iyayenta suka tilasta sai ta auri Audu wanda ba ta son ta aure shi kwata-kwata.

Bayan an tilasta mata ta auri Audu, da yayi kokarin kwanciya da ita ta ki amincewa sai yayi mata fyade inda har ta mutu sanadiyyar hakan.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke Audu da laifin kashe matarsa kwanaki kadan bayan aurensu, kuma akwai yiwuwar zai fuskanci hukuncin kisa idan kotu ta yanke masa hukunci.

Jinjiri ya ce tuni jami’an ‘yan sanda sun dauki gawar marigayiyar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da ta mutu.

Jinjiri ya kara da cewa bayan sun gabatar da bincike akan mai laifin, a karshe ya amsa laifinsa.

“Da misalin karfe 4 na dare, naje domin na kwanta da ita a matsayina na mijinta, amma taki amincewa, ni kuma nayi amfani da karfina na kwanta da ita.” Cewar Audu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce har yanzu suna cigaba da gabatar da bincike akan lamarin kafin su kai ga mika maganar gaban alkali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here