Tashin hankali: An tsinci gawar kanin dan majalisa a bayan motar dan majalisar

0
7864

Mutanen jihar Ebonyi sun tashi da wani sabon al’amari da ya girgiza kowa, bayan an gano gawar dan uwan dan majalisa da yake wakiltar Ebonyi ta Arewa, Victor Aleke, a cikin motar dan majalisar.

Marigayin mai suna Samuel Aleke, an ruwaito ya bar gidanshi ranar Asabar 23 ga watan Mayu, 2020 da Yamma, kuma tun daga wannan rana ba a kara ganinshi ba har sai ranar Lahadi 24 ga watan Mayu, inda aka tsinci gawar tashi a bayan motar dan uwanshi a kan babbar hanyar Abakaliki zuwa Afikpo.

Samuel Aleke

A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabanshi kuma daya daga cikin dangin dan majalisar wanda ya nemi a boye sunan shi ya bayyana cewa marigayin ya bayyana matarshi cewa zai je wajen abokinshi ya karbo abin jin kida na kunne.

Mutumin ya bayyana cewa bayan shafe awanni ba ta ga dawowarshi ba, matar ta bayyana halin da ake ciki, inda aka fitar neman shi amma ba a ganshi ba sai ranar Lahadi da aka tsinci gawarshi a bayan motar dan uwanshi da raunika a jikinshi.

A cewar mutumin, basu taba tunanin cewa ranar Asabar dinnan ita ce rana ta karshe da iyalan shi za suyi masa kallon karshe ba, inda ya bayyana cewa marigayin ba ruwanshi, baya shiga sabgar da ba tashi ba.

Ya bayyana cewa tuni an sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki, sannan ya kara da cewa za su bi duk wata hanya dan tabbatar da adalci akan kisan shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa ‘yan sanda sun gano gawar marigayin a kan babbar hanyar Abakaliki zuwa Afikpo.

Ta ce: “Rahoton da muka samu ya nuna cewa marigayin yace zai je ya karbo abin jin kida sannan ya siyo katin waya.

“An kai gawar marigayin dakin ajiye gawa domin fara bincike a kanta a gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here