Tashin hankali: A karon farko Shekau ya rushe da kuka, ya roki Allah ya kare su daga harin da sojoji ke kai musu

0
160

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya koka a wani faifan sautin muryarshi da ya fitar, inda ya fara rokar Allah ya ya kare su daga harin da sojoji ke kai musu.

A kwanan nan, dakarun yakin Najeriya sun kai hare-hare da dama kan ‘yan kungiyar ta Boko Haram, inda suka samu nasara a kansu.

Sakon muryar da aka fitar mai tsawon minti 1 da dakika 22, wanda jaridar Daily Nigerian ta samu, shugaban kungiyar ta Boko Haram yayi magana cikin harshen Kanuri, inda ya dinga rokar Allah ya kare su daga harin da dakarun na Najeriya ke kai musu, inda ya ce suna cikin wani hali a wannan watan na Ramadana.

“Idan har shaidanci ne da rashin imani sojojin Najeriya suke nuna mana, Allah ka kare mu. Ya Allah ka kara mana imani da son addininka.

“Mun fita daga kungiyar Izala, Tijjaniyya, Shi’a domin mu bauta maka yadda ya dace; mun guji iyayenmu duka domin addininka.

“Saboda addininka ne muke yanka mutane, amma yau suna kokari su canja mana ra’ayi. Ya Allah kaji tausayinmu a cikin wannan wata naka na Ramadana.

“Ya Allah ka bamu nasara akan abokanan gabar mu. Yaku ‘yan uwa, dan Allah ku taimakeni da addu’a. Hakan ba wai yana nufin ina cikin fushi bane.

Da yake magana akan wannan bayani na Shekau, Bulama Bukarti, babban lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, wanda ya kwashe shekaru yana nazari akan ‘yan kungiyar ta Boko Haram, ya ce: “Wannan shine karo na farko da muka fara jin Shekau yana kuka.”

A cewar Bulama wannan magana ta Shekau ta tabbatar da cewa wani abu na faruwa da shugaban kungiyar ta Boko Haram.

“Shekau din da muka sani bashi da kunya, dan iskane, marar imani, wanda bashi da aiki sai yiwa mutane barazana. Wannan magana tashi na nuni da cewa akwai wani abu marar dadi da yake faruwa da kungiyar ta Boko Haram. Duk abinda zai saka Shekau yayi kuka wannan abu ba karami bane, kuma ina ganin hare-haren da sojojin Najeriya ke kai musu ne.

“Sojojin sun saki labarai da hotuna akan nasarar da suka samu akan mayakan na Boko Haram. Hakan shi ya saka Shekau kokawa akan hare-haren. Yana ganin dakyar za su sha a wannan karon,” cewar Bulama.

Sai dai kuma yace wannan magana ta Shekau ba tana nufin cewa shugaban ‘yan Boko Haram din yana so ya mika wuya ko kuma ya sasanta da gwamnati bane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here