Tabbas Allah sai ya sakawa talakawan Najeriya akan yadda muka mulke su – Sanata Dino Melaye

2
1083

Tsohon Sanatan jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, yayi Allah wadai da duka shugabannin Najeriya na da dana yanzu ciki kuwa har da shi kanshi, inda ya ce “Allah sai ya sakawa talakawan Najeriya akan yadda suka tafiyar da Najeriya.”

Dino ya bayyana hakane a martanin da yake bayarwa kan yunwa da ta addabi ‘yan Najeriya a yayin da suke kulle a cikin gida ba tare da an basu wani tallafi ba, yayin da gwamnatin kasar ke kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar ta Coronavirus.

Melaye ya ce:

“Duk wani shugaba da yake mulki a Najeriya a yanzu ko kuma a baya ciki hadda ni, mun bawa Najeriya kunya. Mun sayar da danyen mai na tsawon shekaru 64, amma mun kasa ciyar da al’ummar Najeriya na tsawon mako biyu kacal. Tabbas Allah sai ya sakawa talakawan Najeriya. Lokaci yayi da komai zai canja.

2 COMMENTS

  1. That’s true..this is the reason why (poor and the needy),we never forgive our Nigerian political leaders,but excluding you”Dino Melaye”..i apologise you best on your good mind..how i wish you to be a muslim..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here