Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bukaci a bude Masallatai da Coci a fadin Amurka

0
371

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya umarci gwamnoni da su bude wuraren bauta, inda yace bai kamata ba wasu gwamnonin su bar wuraren zubar da ciki da mashaya a bude amma su rufe wuraren bauta irinsu coci da masallatai.

Duk da annobar coronavirus da ta kashe sama da mutane 95,000 a kasar ta Amurka, a jiya Juma’a ne Trump ya ce yana so duka wuraren bauta da suka hada da coci da masallatai da a bude su a fadin kasar.

Da yake magana akan gwamnonin da suka bar mashaya da wuraren zubar da ciki a bude sannan suka rufe wuraren bauta, Trump ya ce:

“Hakan ba daidai bane, ina kira da a bude duka wuraren bauta.”

“Idan akwai wata tambaya su kirani, amma ina tabbatar muku baza su dace ba da wannan kiran,” cewar Trump ga gwamnonin.

“Ya kamata gwamnoni suyi abinda ya kamata, su bar wurare masu muhimmanci na bauta a bude a karshen wannan satin.”

“Idan basu bude ba zanyi watsi da su duka.”

“A Amurka muna bukatar addu’a da yawa,” cewar Donald Trump kafin ya bar dakin taron na fadar shugaban kasa.

Trump ya shiga wannan dakin taro ne inda ya sanar da hanyoyin da cibiyoyin magance manyan cutukasuka gindaya ga shugabannin jihohi domin bude wuraren bauta.

“Muna so wuraren bautar mu a bude su,” ya ce, “na dauke su da matukar muhimmanci, kun san akwai wuraren da basu da muhimmanci amma an bar su a bude, amma an rufe wuraren bauta.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here