Sultan Hassanal Bolkiah: Takaitaccen labarin Sarkin da yafi kowa kudi a duniya

0
1239

Sarkin Brunei, Hassanal Bolkiah, yana daya daga cikin Sarakai masu kudi a duniya. A rahoton da Insider ta bayar, ya taba mallakar dala biliyan arba’in ($40bn), kimanin N15,500,000,000,000.

Wasu daga cikin abubuwan da yafi so a rayuwarshi sun hada da gudun mota da tsakar dare a cikin babban birnin kasar, da kuma kashe dala dubu ashirin ($20,000), kimanin naira miliyan takwas a kudin Najeriya, wajen yin aski kawai.

Sultan Hassanal Bolkiah | Photo Source: Facebook

Sarkin dai ya gaji mahaifinsa ne, Sultan Omar Ali Saifuddien, wanda yake da ‘ya’ya guda goma daga mata daban-daban.

Mahaifin Bolkiah ya sauka daga karagar mulkin kasar a shekarar 1967, inda ya bashi ita a lokacin da yake makarantar sojoji ta kasar Ingila dake Sandhurst.

Bayan shekara daya, Bolkiah ya hau karagar mulkin bayan ya kammala karatunsa. Ana yi masa inkiya da Sarkin yaudara, saboda yana taba harkar mata duk kuwa da cewa da aurenshi.

Fadar shi tana da girma sosai, wanda ya zana fadar wani fitaccen mai zane ne da yayi suna a duniya Architect Leandro Locsin. A wani rahoto da Guiness ta taba fitarwa, fadarsa din ita ce tafi kowacce fada girma a duniya.

Hoton fadar Sultan Hassanal Bolkiah | Photo Source: Facebook

Wani abu game da shi kuma shine, danginsa sune suka saye rabin motocin kamfanin Rolls-Royce, inda a yanzu haka shine mutum na farko da yafi kowanne yawan wannan motar a duniya, inda rahotanni suka bayyana cewa yana da akalla guda 500.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here