Sule Lamido ya caccaki Atiku Abubakar kan ikirarin da yayi game da jam’iyyar PDP

0
1121

A jiya ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar akan ikirarin da yayi akan jam’iyyar PDP.

Atiku, wanda ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ranar Alhamis dinnan yayi wata magana a shafinsa na Twitter, inda ya ce: “PDP ta zama misali irin wanda kundin tsarin mulki ke bukata don dorewar dimokuradiyya a Najeriya.

“Ina addu’ar Allah yasa irin tsari da bin doka da jam’iyyarmu take da shi ya kasance abin koyi ga sauran jam’iyyu. Idan babu doka da oda jam’iyya baza ta iya daidaita lamuran Najeriya ba,” ya ce.

Atiku ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kwamitin zartarwa ta jam’iyyar APC ta kasa ta rushe kwamitin ayyuka ta kasa (NWC) kan rikice-rikicen da ke faruwa a cikin jam’iyyar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar dai yayi takarar neman tikitin takarar shugaban kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2014.

Bayan gabatar da zaben fidda gwani a jihar Legas, Atiku ya zo na uku, inda tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama na kusa da Buhari.

A watan Disambar shekrar 2017, Atiku ya dawo jam’iyyar PDP, inda ya fito takarar shugaban kasar a shekarar 2019.

Da yake mayar masa da martani, Sule Lamido ya karyata ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasar, inda ya ce: “Ina ganin PDP ba ta da bakin da za ta yi irin wannan ikirarin.”

Lamido ya kara da cewa: “Abinda kawai buke bukata shine muyi tunani akan yadda muka tafiyar da ayyukanmu da zamu iya alakanta wannan magana. Tambayar kanmu ne zai tabbatar da irin halayen mu.

A shekarar 2018, Atiku Abubakar ya doke mutane 11 a zaben fidda gwani da aka gabatar, ciki kuwa hadda Sule Lamido.

Daily Trust ta bayyana cewa su biyun suna daga cikin jiga-jigan wadanda ake sa ran za su fito takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here