Ma’auratan da suka shekara 19 suna tare sun rabu sanadiyyar bidiyon rawa da matar ta wallafa a shafukan sadarwa wanda ya jawo hankalin mutane da dama musamman a yankin Arewacin Najeriya.
A yayin bikin sallar idi, matan arewa sun dauki gasar rawa da mazajensu su wallafa a shafukan sadarwa tare da sanya alamar #DancingForHusbands.
Wannan gasa dai ta bawa mutane da dama sha’awa a shafukan sadarwa. Sai dai kuma a jiya wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa daya daga cikin matan da suka wallafa wannan bidiyo na rawa a shafin sadarwar mijinta ya sake ta.
Ya kara da cewa matar ita ce daya tal a gidan shi, wacce suka yi aure shekaru 19 da suka wuce, amma ya sake ta saboda ta wallafa wannan bidiyo a shafukan sadarwa.
Sanusi Bature ya ce: “Innalillahi Wa’inna Ilahi Raji’un.
‘Yanzun nan nake samun labarin daya daga cikin iyayen gidana ya saki matarshi akan ta wallafa bidiyon rawa a shafukan sadarwa jiya da daddare.
“Babban abin takaicin shine, auren nasu yanzu shekara 19 kenan da yi suna da ‘ya’ya 3 tare, kuma ita kadai ce matarshi.
“Allah ya kyauta.”
Ga wasu daga cikin bidiyon da muka samo muku a shafin Facebook:
Wlh sakin ta da yayi min daidai domin yin hakan ba mutumci bane