A jiya Juma’a ne 9 ga watan Yuli, 2020, shugaban babbar jam’iyya mai mulki ta APC, na karamar hukumar Ese-Odo dake jihar Ondo, Samuel Olorunwa Ajayi, ya sauka daga mukaminsa sannan ya fita daga jam’iyyar baki daya.

Wannan dai ya zo ne makonni kadan a gabatar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na gwamnan jihar.

Ajayi wanda ya gabatar da takardar yin murabus dinsa a sakatariyar jam’iyyar jihar, ya kuma bayyana cewa ya bar jam’iyyar ya koma jam’iyyar PDP.

Ajayi dai yana da kyakkyawar alaka da mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi, wanda a ‘yan kwanakin nan ya bar jam’iyyar ta APC ya koma PDP, Ajayi shine mutumin da ya karbi takardar murabus din mataimakin gwamnan a lokacin da ya bar jam’iyyar APC watan da ya gabata.

Agboola Ajayi suna takun saka da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu kuma ya nuna burinshi na fitowa ya kara da shi a watan Oktobar wannan shekarar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here