Shugaba Buhari ya bayyana ainahin halin da Najeriya ke ciki

0
386

A cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wata ganawa da yayi da kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki a jiya Talata 30 ga watan Yuni, ya ce Najeriya na cikin wani irin mummunan yanayi na rashin cigaba.

Taron wanda ya samu halartar, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Boss Mustapha, shugaba Buhari ya ce akwai bukatar a gyara yanayin tattalin arzikin Najeriya, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya ce yawancin ‘yan Najeriya talakawa ne, wadanda a yanzu haka matsalar tattalin arziki da annobar coronavirus ta fi addaba.

Shugaban kasar ya ce: “Muna da kasa ne wacce talakawa suka fi yawa, rashin abubuwan more rayuwa, rashin matsugunnai da kuma matsalar tatattalin arziki da yanzu cutar COVID-19 ta kara sakowa a gaba, da kuma rushewar bangaren man fetur.

A jiya Talata 30 ga watan Yuni ne dai shugaban kasar ya shiga ganawar da mataimakinsa Osinbajo da kuma shugaban ma’aikatansa Ibrahim Gambari.

Taron wanda aka sanar da shi a shafin gwamnatin tarayya na Twitter, ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayyar, Bos Mustapha.

Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da kwamitin shawari akan matsalar tattalin arziki, wacce Bismarck Rewane yake jagoranta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here