Shigar tsiraicin da kuke yi ne yasa maza ke yi muku fyade – Likita ya dora laifin fyade akan mata

2
2009

Wani mai amfani da shafin Twitter ta wallafa hirar da tayi da wani likita. Hoton da ta wallafa ya nuna yadda likitan ya mayar da abin wasa ya dora laifin akan yanayin yadda mata suke shigarsu.

A hirar ta su, likitan ya bukaci mata su dinga sanya manayn kaya, inda yake ganin hakan ita ce hanyar da za a rage samun yawan fyade. Ya kara da cewa “a lokuta da dama kune kuke jawowa kan ku.”

Photo Source: @sassy_Ayom Twitter Page

Mutane na ta faman magana akan fyade ne tun bayan fyaden da aka yiwa dalibar jami’a Uwa Omozuwa kuma aka yi mata kisan gilla a cikin coci.

KU KARANTA: Yadda aka yiwa dalibar jami’a kisan gilla bayan anyi mata fyade ta karfin tsiya a cikin coci

Sai dai kuma maganar da likitan yayi ta bawa masu amfani da shafin na Twitter mamaki, inda suke ganin yaya lamarin yake dangane da matan da yake mu’amala da su.

Ta ce: “Nayi rubutu akan fyade yau da safe a WhatsApp, wannan kuma shine martanin da wani ya dawo mini da shi. Mutumin da yake da ilimi kuma likita, muna aiki a waje daya ne ma.

Likitan ya ce:

“Ku koyi yadda ake saka kaya na mata. Ku dinga sanya babbar riga. Ku rufe tsiraicin ku. Idan kuka bude jikinku, hankalin kowa zai dawo kan su ne. Tilasta mace ta kwanta da mutum ba abu bane mai kyau, amma na tabbata a lokuta da dama sune suke jawo wa kansu.

Post Source: @sassy_Ayom_ Twitter Page

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here