Sherin Khankan: Mace ta farko da take jan Musulmai Sallah ta kuma yi wa’azi a Masallaci a kasar Denmark

0
229

An haifeta a shekarar 1974, iyayenta duka kiristoci ne, Sherin Khankan, ita ce mace ta farko da ta zama limamiya a kasar Denmark. A shekarar 2016, ita da wata kungiyar Musulmai, sun samar da Masallacin Mariam a Copenhagen – daya daga cikin masallatai na farko a nahiyar Turai da mace take jagoranta kenan.

“Komai yana farawa da yanayin magana ta al’umma ne,” Sherin ta gayawa Al-Jazeera. “Idan har bakin mutum bawa ya zama mutum na farko da zai fara kiran sallah, wannan wata mu’ujiza ce, ganin yadda ake yiwa bakar fata wani irin kallo a wancan lokacin da yanzu.” Canji ba wani sabon abu bane a Musulunci, cewar ta.

Masallacin dai yana koyar da abubuwa guda uku ne:

Na farko yana koyar da cancantar mata su jagoranci Musulmai a Masallaci, ma’ana suyi limanci; gyara akan aurace-aurace da kuma bayar da ikon saki a duk lokacin da mace taga baza ta iya zama ba. Tun bayan bude masallacin a cikin aure 50 da aka yi a masallacin, kusan rabi duk sun yarda da wannan doka.

“Masallacin Mariam ya dace da yanayin zamani na yanzu. Mutane na zuwa daga sashe daban-daban na duniya su hadu da mutane kala-kala,” cewar Khankan. “Baza mu iya tilasta wadannan mutane suyi imani da abinda muka yi imani da shi ba. Masallacinmu ya dace da mutanen wannan lokaci da suke Musulmai amma kuma suke zaune a kasar da ba ta Musulmai ba.”

Shekaru hudu bayan bude Masallacin, sun samu wasu ma’aurata da suke son auren jinsi. Duk da dai shugabannin masallacin basu yi magana akan auren ba, amma basu yanke hukuncin daurin auren ba.

“Mun yarda da soyayya. Amma akwai banbanci tsakanin yin abu da kuma kyale abin. Yanzu dai bamu yi auren ba, amma zai iya yiwuwa nan gaba ayi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here