Shekara daya na kwashe ina luwadi da mahaifin matata, kuma ina son shi fiye da matata – Miji ya bayyana sirrin shi

0
446

Wani mutumi wanda ya bayyana cewa yana son matarshi ya bayyana cewa ya kwashe shekara daya yana kwanciya da mahaifin matarshi, ma’ana yana luwadi dashi, inda yace bai tunanin zai iya daina kwanciya dashi, saboda yafi jin dadi idan ya kwanta da shi.

A yayin da ya roki kada a bayyana sunanshi, mutumin ya bayyana haka a wata wasika da ya aikawa Joro Olumofin, masani kan zamantakewar ma’aurata, inda ya bayyana mishi cewa shi da sirikin nashi duka ‘yan luwadi ne amma ya kasa sanarwa da matarshi.

A cewar shi yafi jin dadin kwanciya da mahaifin matar tashi fiye da matarshi ta sunna, yace yana zaune da matarshi ne kawai saboda ta kula da ‘ya’yansu.

“Na jima ina dauke da wannan nauyin a zuciyata, har ya kai matsayin da na kasa daina tunanin shi.

“A watan Disambar shekara da ta gabata, mijin matata ya gayyace ni wajen biki, inda yace zan hadu da wani mutumi da zai bani aiki.

“Naje wajen bikin, tun lokacin dana ga yana mu’amala da jama’a na gane cewa shi dan luwadi ne, sannan naga yadda yake taba jikina da yadda yake kallona.

“Zancen gaskiya nima dan luwadi ne, amma ina matukar son matata, sai dai abubuwa sun faru da sauri wanda ban taba tunani ba, kuma bazan iya fada mata ni dan luwadi ne ba haka yasa na aureta, ina matukar son yara.

“Ina matukar son matata, amma mahaifinta yafi kwanciya a zuciyata. Ina matukar son kasancewa kusa dashi, ba wai dan yana da kudi ba, kwarai yana saya mini abubuwa, amma ina son shi sosai.

“yadda yake kallona a wannan rana yana lashe baki ya saka dole sai da muka kwanta bayan wannan biki.

“Komai namu iri daya ne, baya son aure amma an takura shi yayi auren dole, a lokacin da yake saurayi anfi sakawa ‘yan luwadi ido fiye da yanzu. Ina matukar son shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here