Saurayi ya yiwa budurwarshi yankan rago saboda tace ta gaji da soyayya da shi

0
251

Wani saurayi mai suna Tishko Ahmed Shabaz, mai shekaru 23, ya yankewa budurwarshi kai a lokacin da ta je gidanshi za ta dauki kayanta bayan ta daina soyayya da shi.

Budurwar ‘yar shekara 17 mai suna Wilma Andersson, sun kwashe shekara biyu suna soyayya kafin daga baya ta ce ta daina soyayya da shi.

Wilma Andersson budurwar da aka yankewa kai

An nemi budurwar a ranar 14 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata an rasa, kafin daga baya ‘yan sanda suka samu wani sashe na jikinta, sai aka gano cewa kanta ne.

‘Yan sandan sun cafke Ahmad suka tsareshi a wajensu, bayan sun gabatar da bincike a cikin gidanshi sun ga jini a ciki.

Wilma Andersson budurwar da Ahmad ya yankewa kai

A yadda rahotannin kotu suka bayyana, ‘yan sanda sun gano kan mutum a cikin wata karamar jaka, an nade a cikin leda a ranar 28 ga watan Nuwamba, hakan ya kawo karshen nemanta da ake yi, inda kuma suka fara sabon bincike akan kisanta da aka yi.

‘Yan sanda sun bayyana cewa an samu shaidar DNA din Shabaz dana Wilma a jikin wuka, sannan kuma an samu shaidar yatsunsa a jikin jakar da aka sanya kanta a ciki, amma har yanzu ba a san inda gangar jikinta take ba.

Masu kai kara sun bayyana cewa an sha kama shi da laifuka da dama bayan mutuwar Wilma.

Shabaz Ahmad, saurayin Wilma da ya yanke mata kai da wuka

Shabaz wanda yake dan asalin kasar Iraqi ne, ana zarginshi da laifin kisan kai, kuma za a fara shari’ar shi a ranar 26 ga watan Mayu, sai dai kuma ya musanta kashe budurwar ta shi.

Yaki yayi magana a lokacin da ‘yan sanda suke yi masa tambayoyi a watan Afrilu. Haka kuma da yake magana da manema labarai ya ce, “idan har ni na kasheta babu yadda za ayi na yanke mata kai.”

Mahaifiyar Wilma ta sanar da batan budurwar a ranar 14 ga watan Nuwamba, inda mutane 5,000 da suka hada da ‘yan sanda, masana a fannin bincike, da kuma ‘yan sakai suka bazama nemanta.

Mrs Andersson ta sanar da gidan Talabijin cewa tayi ta tambayar Shabaz akan Wilma, amma sai yace mata rikici ne kaiwa ya hada su kuma ta fita daga gidan shi.

Rigar Wilma da jakarta suna cikin gidan, kuma mahaifiyarta tace babu yadda za ayi Wilma ta fita daga gidan ba tare da rigarta da jakar ba.

Kawayen Wilma sun bayyana cewa Shabaz ya kware wajen juya Wilma, inda suka ce shine yake gaya mata kayan da za ta saka da kuma inda za taje. Sun ce taje gidan shi ta dauko kayanta ne, inda tun daga nan aka neme ta aka rasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here