Saurayi ya shiga tashin hankali bayan ya gano budurwar da zai aura kanwarshi ce da suke uba daya

0
999
  • Wasu masoya sun shiga rudani sosai, bayan sun gano cewa su ‘yan uwan juna ne da suka hada uba daya
  • Masoyan wadanda suke ‘yan asalin kasar Kenya sun nuna damuwarsu matuka, inda suka ce da kyar za su iya cigaba da soyayya da wasu
  • Budurwar ta ce daga lokacin babu ita babu soyayya saboda tana tsoron ta kara soyayya da wani da suke da dangantaka dashi

An bukaci wani saurayi mai suna John Njoroge ya dakatar da shirin auren da yake yi ga budurwarsa Rose Wanjiku, bayan an gano cewa su ‘yan uwan juna ne na jini, bayan ta bayyana asalinta ga iyayen saurayin.

Da yake bayyana irin halin da ya shiga sanadiyyar haka, Njoroge ya ce an sanar da shi cewa Wanjiku kanwarshi ce wacce suke uba daya.

John ya bayyanawa gidan talabijin na Kameme TV dake kasar Kenya cewa;

“Bayan na kai ta ga iyayena su gana, an sanar dani cewa mahaifina yana da wata daban, inda aka sanar dani cewa mu ‘yan uwan juna ne.”

Njoroge wanda ya fara soyayya da budurwar bayan ta sayi takalmi daga wajen shi, ya bayyana cewa soyayyar da yake yiwa budurwar tayi yawa a zuciyarshi.

A na ta bangaren, Rose ta bayyana tsoron kara soyayya da wani kuma, inda ta ce:

“Ba zan sake soyayya ba daga yanzu har abada, saboda ina tsoron kada sai abu yayi nisa shi ma ace dan uwana ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here