Saurayi ya mallaki kamfanin man fetur, bayan shafe shekaru yana aikin gadi

0
622

Wani saurayi da aka bayyana sunan shi da AD Patrickson ya bayyana tarihin nasarar da ya samu a rayuwa akan yadda ya kai matsayin da ya mallaki kamfanin man fetur, bayan shafe shekaru yana aiki a matsayin mai gadi a wani kamfanin man fetur.

Babu abinda zai iya ja da aiki tukuru da kuma soyayya akan abu. Patrick ya ce kafin ya kawo wannan matsayi sai da ya hakura da duk abinda yake da shi. Haka kuma ya kara da cewa hakane kuma ya sanya ya koma karatu.

AD Patrickson a lokacin da yake aikin gadi | Hoto: MSN.com

Kada ka taba zama wanda ba a cin moriyar sa, masana sun bayyana cewa sai da ya taimakawa kasar ta Kamaru, a lokacin da yake fafutukar neman sa’a a rayuwa.

A karshen abinda ya rubuta a shafinsa na LinkedIn, ya shawarci kowanne mutum mai buri a rayuwa da kada ya cire rai da rabo, inda ya ce dan takin kalilan ne.

AD Patrickson lokacin da ya mallaki kamfanin man fetur | Hoto: MSN.com

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here