Saurayi ya kashe kishiyar mahaifiyarshi da take zuwa masa kullum a mafarki

0
422

A ranar Juma’a ne wata kotun majistire dake zaune a Abakaliki, ta tura wani mai suna Elom Maduka, mai shekaru 38 zuwa gidan gyaran hali, bayan kama shi da laifin kashe kishiyar mahaifiyarshi mai suna Mrs Augustina Odio.

An ruwaito cewa mutumin ya bayyana cewa matar tana zuwa mishi a mafarki tana ce masa ita ce dalilin da ya saka ya kasa samun cigaba a rayuwa.

Saurayin ya ja ta zuwa gonarta, inda ya sassarata da adda.

A rahoton da Punch ta ruwaito, mutumin ya aikata laifin a kauyen Amohu dake karamar hukumar Ishielu cikin jihar Ebonyi.

An gurfanar da mai laifin a gaban kotu da laifin kisan kai.

Dan sandan da ya gurfanar da mai laifin a gaban kotun, ASP Mathias Eze, ya sanar da kotun cewa laifin ya sabawa sashi na 319 na kundin tsarin mulki na jihar Ebonyi na shekarar 2009.

Ya ce: “Kai, Elom Odio Maduka, a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2020, a Amohu Ezillo kayi sanadiyyar mutuwar Augustino Odio, mai shekaru 50, ta hanyar sassarata da adda a kai da kafa, saboda haka kayi laifi wanda ya sabawa sashe na 319 na kundin doka ta jihar Ebonyi na shekarar 2009.”

Babu wanda ya tsayawa wanda ake karar dai a kotu, haka kuma ba a bayar da belin shi ba.

Alkalin kotun, Nnenna Onuoha, ya umarci a kai shi gidan yari dake Abakaliki, inda za a mika kararshi zuwa ga ofishin darakta na yankewa mutane hukunci domin daukar hukuncin da ya dace a kanshi.

A karshe ya daga cigaba da sauraron karar har zuwa 15 ga watan Yuli, 2020.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here