Saurayi ya kashe kannanshi mace da namiji a wannan watan kan sun zuba suga a cikin kayan buda baki

0
189

Yanzu duniyar nan ta zama abin tsoro, inda abubuwa masu daure kai suke faruwa. Mutane na aikata abubuwa na ban tsoro.

Abubuwa marasa dadin ji na ta faruwa a kasashen Musulmai, kwanan wani lamari ya faru a Peshawar dake kasar Pakistan, inda suga ya zama dalilin da ya saka wani ya aikata kisan kai.

Abin takaici a wannan lokacin shine, wannan annobar ta sanya komai ya canja a duniya, hatta watan Ramadana na wannan shekarar ya fita daban da sauran, kullum lamari kara lalacewa yake.

Kamar yadda kafafen sadarwa na kasar suka ruwaito, a farkon makon nan, wani mutumi ya kashe ‘yan uwanshi akan wani dan rikici da ya hado su. Lamarin ya faru a Peshawar, kuma mutumin ya shiga wasan buya da jami’an tsaro tun bayan faruwar lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin mai suna Muhammad Ishaq, yana zaune a Mithra ne dake garin na Peshawar. A farkon makon nan kanwarshi mai suna Mismat da kaninshi Hussain sun zuba suga a cikin kayan buda bakinsu ba tare da sun sanar dashi ba. Kafin kace meye wannan tuni har rikici ya tashi a tsakaninsu, inda a karshe ya kashe su duka su biyun.

Cikin fushi ya tashi ya dauko bindiga ya harbe su duka biyun, bayan ya kashe su sai ya gudu kafin ‘yan sanda su je wajen.

Da yake magana akan lamarin, jami’in hukumar ‘yan sanda ya bayyana cewa makwabtan mutumin ne suka dauki gawarwakin Mismat da Hussain zuwa asibiti.

Ya zuwa yanzu dai an aika jami’an hukumar ‘yan sanda su kamo Ishaq duk inda yake.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here