Saurayi ya kashe budurwarsa kan ya nemi yayi lalata da ita taki amincewa

0
835

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Shagbada Erigga, da laifin kashe budurwarsa mai shekaru 30, mai suna Happiness Winfred a Oritoke, Ibadan Jihar Oyo.

Da yake yiwa manema labarai bayani, kwamishinan ‘yan sandan jihar (CP) Joe Nwachukwu Enwowu, ya bayyana cewa an kama Erigga bayan wani mai suna Agu Benson, mai shekaru 25, ya kai kara a ranar 25 ga watan Yuni, 2020, cewar ya ga gawa a cikin rijiya a cikin gidansu.

“Binciken da ‘yan sanda suka yi ya taimaka an kama Shagbada Erigga wanda yake makwabcin Benson ne.

“Happiness ta bar gidansu ranar Lahadi 21 ga watan Yuni, 2020, amma an tsinci gawarta a cikin rijiya a ranar 25 ga wata. Sai dai kuma tunda har mai laifin ya amsa laifinsa, za mu gurfanar da shi a gaban kotun.”

Da yake magana da manema labarai, wanda aka kama da laifin ya ce ya kashe Happiness ne saboda taki amincewa yayi lalata da ita.

“Ba a son raina na kashe ta ba, marigayiyar budurwa ta ce, amma tun da muka fara soyayya ba ta taba bari na kwanta da ita ba ko sau daya.

‘A wannan ranar da lamarin ya faru, muna wanka tare, sai nake tambayarta dalilin da ya saka taki barina na kwanta da ita, sai ta fara yi mini masifa tana daga mini murya, ni kuma sai na mare ta, abin mamaki sai ita ma ta rama, ni kuma sai na nausheta sau uku a baki da daya a wuya.

“Abinda na sani kawai shine, kawai ta fadi a kasa ta ce ga garinku nan. A lokacin dana ga ta mutu sai na dauki gawarta na jefa cikin rijiyar dake gidanmu, saboda na tsorata sosai, kuma bana so mutane su zarge ni.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here