Saurayi da budurwa sun kashe kansu bayan an daga daurin aurensu saboda annobar Coronavirus

0
123

Saurayi da budurwa dake garin Telangana, sun kashe kansu saboda daga daurin aurensu da aka yi sanadiyyar annobar coronavirus da ta hana kowa sakat.

Pendur Ganesh mai shekaru 22 da Soyam Seethabai 20 sun kashe kansu ta hanyar maganin kwari a wata gona dake kauyen Kannapur.

A rahoton da ‘yan sanda suka bayar, Ganesh wanda yake manomi ne da budurwarshi da suka hadu a kauyensu suna soyayya tsawon shekaru da yawa. Anyi musu baiko watanni kadan da suka wuce, inda aka bayyana daurin aurensu wata na gaba.

Sai dai kuma duka dangin ango dana amarya sun amince da daga daurin auren, sanadiyyar dokar hana zirga-zirga da aka sanya. Hakan ya sanya masoyan suka yi fushi.

Bayan an kara daga dokar hana fitar, sai saurayi da budurwar suka shiga cikin wani hali.

“Duka dangin mijin dana matar sun amince akan daga bikin nasu, saboda dokar hana zirga-zirga da aka saka a Telangana. An gano gawarwakinsu a wata gona. Mun kai su asibiti domin ayi bincike a kansu,” cewar jami’in dan sanda M. Vijay.

Dokar hana zirga-zirga dai da aka sanya a garin na Telangana a ranar 22 ga watan Maris, ta janyo an daga auren dubunnan mutane a garin, inda gwamnati ta hana taron jama’a, a kokarin ta na dakile yaduwar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here